A DAINA ƁATANCI GA MANZON ALLAH صلى الله عليه وسلم DOMIN SAMUN ZAMAN LAFIYA daga MUSULMI SOLIDARITY FORUM, SOKOTO

May 19, 2022 - 21:32
 64
A DAINA ƁATANCI GA MANZON ALLAH صلى الله عليه وسلم DOMIN SAMUN ZAMAN LAFIYA daga MUSULMI SOLIDARITY FORUM, SOKOTO

بسم الله الرحمن الرحيم 

A DAINA ƁATANCI GA MANZON ALLAH صلى الله عليه وسلم DOMIN SAMUN ZAMAN LAFIYA

daga MUSULMI SOLIDARITY FORUM, SOKOTO

[Majalisar Haɗin Guiwar Musulmi, Jahar Sokoto]

Address: Rabiɗa Office, AbdurRahman Al-Zaid, Sokoto 

Phone No: 07034326424

Talata, 16 ga Shawwal , 1443 Hijriyyah / 17 ga Mayu, 2022

1. Majalisar Haɗin Gwiwar Musulmi ta Jihar Sokoto, a matsayin ta na inuwar da ta tattara Limamai, Malamai, Masu Wa'azi, Ƙungiyoyi da Cibiyoyin Addinin Musulunci da Ɗarikun Sufaye a wannan jihar, ta na bibiyar abubuwa marasa daɗi da suka faru a ranar Alhamis ɗin da ta gabata 11 ga Shawwal, 1443 bayan Hijira (12.05.2022 Miladiyya) a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto da kuma abubuwan da suka biyo baya tare da nuna matuƙar damuwa kuma ta na bayyana matsayinta kamar haka:

2. Lamarin ya samo asali ne a lokacin da wata ɗaliba Kirista mai suna Deborah Yakubu ta tura saƙon murya a zauren WhatsApp na ɗalibai saboda wasu daga cikin Musulmin zauren suna saka wasu bayanai na Musulunci a ciki. A cikin saƙon da ta yi da harshen Hausa, wanda kuma ya yaɗu sosai, an ji ta tana zagin Addinin Musulunci tare da ƙundumawa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) zagi ko ashar, tana mai alfahari da cewa ba abin da zai faru da ita, duk da gargaɗin da ƙawayenta suka yi mata. Wannan aika-aika shi ne mafi girman tsokanar da wani zai iya yi ga duk wani Musulmin da ya ke da ƙwayar zarra ta imani a zuciyarsa. Hakanan kuma, kamar yadda ya ke cikin saƙon murya wanda aka yaɗa, mai kulawa da ɗakunan kwanan ɗalibai ta sha gargaɗinta a kan yadda ta ke yin kalamai na rashin hankali da ka iya kawo fitina!

3. Wannan rashin hankali da katoɓara ya haifar da tarzoma daga dalibai, inda suka nuna adawa ga wannan mummunar tsokana a cibiyar Daular Usmaniyya. Wannan ya kai ga rasa ran wannan dalibar a lokacin zanga-zangar.

4. Don haka muna yin Allah-wadai da kakkausar murya ga kowane irin ɓatanci ga Shugabanmu, wanda ya fi kowa daraja, Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) daga kowane mutum ko wanene shi!

5. Duk da tsananin muni da girman wannan laifi, muna kira ga dukkan Musulmi da kada su ɗauki doka a hannunsu, su ƙyale hukumomin da abin ya shafa su yi abinda ya dace ga doka ga irin wannan lamari.

6. Wannan dai ba shi ne karon farko da wani Kirista, dalibi ko waninsa, ya ke yin gangancin yin kalaman ɓatanci ga Shugabanmu Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ko ƙoƙarin yin ɓatanci ga Alkur'ani Mai girma a ciki da wajen wannan jihar ba, wanda hakan ya ke janyo rikicin addini da asarar rayuka da dukiyoyi kamar yadda aka shaida cikin shekaru talatin (30) da suka gabata. Don dakatar da wannan mummunar ɗabi'a, akwai bukatar haɗa-karfi-da-karfe daga masu ruwa da tsaki domin magance tushen wannan barazana. 

7. Domin cimma abin da aka ambata a sama, ya kamata waɗannan abubuwan su fito fili ga kowa:

i. Duk wani Musulmi na ƙwarai – bisa ga koyarwar Addininsa - ya fi son Shugabanmu Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) fiye da kansa da iyayensa da ‘ya’yansa da dukkan mutane. Ba zai yi shakkar sadaukar da rayuwarsa ba domin kare mutuncin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ba.

ii. Haka kuma, Musulmi suna girmama sauran Annabawa da Manzannin Allah ba tare da nuna bambanci ba, tun daga Annabi Adamu har zuwa Annabi Isa ɗan Maryam (amincin Allah ya tabbata a gare su baki ɗaya). Maganar rashin kunya ko nuna rashin mutunta kowane ɗaya daga cikinsu aikin kafirci ne da yake fitar da mutum daga cikin Musulunci. Shi ya sa babu wani Musulmi na ƙwarai da zai yi tunanin yin haka.

iii. Hukuncin zagin Annabawa (amincin Allah ya tabbata a gare su) shi ne kisa a shari'ar Musulunci. Haka yake ma a cikin Littafin Bible kamar yadda aka ambata a cikin Littafin Firistoci 24 aya ta 10-16; Sarakuna na farko 21 aya ta 10-13 da Sarakuna na biyu surah ta 2 ayoyi 23-25 . Sai dai, aiwatar da wannan hukuncin ya rataya a wuyan hukuma ne.

iv. Tarihi da kuma abubuwan da suke faruwa a yanzu sun nuna cewa yin ɓatanci ga Shugabanmu Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) kamar mutum ya kashe kansa da kansa ne, kuma tabbatacciyar hanya ce ta shiga kuncin rayuwa alal aƙalla, walau a kasashen Musulmi ko inda su ke yan tsiraru. Ai ba mu manta da abinda ya sami malamin makarantar Faransa ba, da ya gabatar da zane-zane na ɓatanci na jaridar Charlie Hebdo ga dalibansa a shekarar da ta gabata.

v. A duk matsalolin ɓatanci da a ka samu a Najeriya cikin shekaru talatin din da suka gabata, Kirista ne ya ke tunzura Musulmi da gangan ta hanyar cin mutuncin Shugabanmu Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ba tare da wani dalili ba, ko kuma ya wulakanta Alƙur'ani Mai girma wanda ke haifar da martani wanda sau da yawa yakan rikiɗe zuwa rikicin addini. Babu wani lokaci da a ka sami wani Musulmi ya yi kalaman batanci ga wani mutum da ake girmamawa a cikin addinin Kiristanci.

vi. Riƙon sakainar-kashi da gwamnatoci da dama a baya suka yi wa wannan lamari mai matukar muhimmanci na ɓatanci ga Manzon Rahama (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) , inda masu tada hankali irin su Rev. Bako a rikicin Kafanchan na 1987, suka tserewa fuskantar shari’ah, yayin da wasu da dama daga cikin Musulmin da ba su ji ba ba su gani ba, suka fuskanci cin zarafi a hannun wasu jami’an tsaro, wannan ya sanya gama-garin Musulmi na kallon matsayin wannan gwamnati da gwamnatocin da suka shude a matsayin wadanda su ka karkata ga kiristoci.

vii. A fili yake cewa, an yi kisan gilla ga Musulmi a Zangon Kataf a shekarar 1991 da 1992; Tafawa Balewa a shekarar 1991, 1993, 1995 da 2001; Yelwan Shendam a shekarar 2004; Zonkwa da Jarkasa a 2011; Mambilla plateau a shekarar 2017; Dura du a Jos a shekarar 2018; An kashe wani dalibi Musulmi a Ijagbo a shekarar 2022 da dai sauransu, amma babu wani mutum ɗaya da aka hukunta kan waɗannan laifuka.

viii. Halin wasu shuwagabannin Musulmi masu saurin yin Allah-wadai da kurakurran da wasu Musulmi ke aikatawa, amma kuma su kame bakinsu gum a duk lokacin da aka keta hurumin Addinin Musulunci, ko a ka salwantar da rayuka da dukiyoyi da mutuncin Musulmi ya na ƙara taɓarbare lamarin. Wannan na daga cikin abinda ke ingiza gama-garin Musulmi zuwa ga ɗaukar hukunci a hannu, domin a fili babu wanda ke da sha'awar kare haƙƙoƙinsu.

ix. Halin da yawa daga cikin shuwagabannin Kirista waɗanda aikinsu ke nuna sun yarda da maganganun ɓatancin da mabiyansu ke yi ta hanyar yin shiru da su ke yi idan an yi ɓatanci ga Manzon rahama (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da ƙin fitowa fili su yi Allah-wadai da irin waɗannan munanan kalamai da kuma rashin koya wa mabiyansu gujewa irin wadannan ayyuka na keta alfarma, haka nan yana ƙarfafa ayyukan ɓatancin da wasu daga cikin mabiyansu ke yi.

8. Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, muna gabatar da bukatu kamar haka:

a. Ya kamata a gaggauta sake duba dokokin da a ke amfani da su wajen hukunta ayyukan ɓatanci, ba a cikin jihar Sokoto kaɗai ba, har ma a faɗin ƙasa baki ɗaya, domin dokokin su dace da girman laifin da aka aikata domin a hana tashin hankali a cikin al'umma da lalata rayuka da dukiyoyi wadanda ba bukatar yin haka.

b. Gwamnatin jihar Sokoto ta biya diyya ga iyalan wadanda jami'an tsaro suka kashe da kuma jikkata a yayin zanga-zangar lumana a ranar Asabar 13 ga Shawwal, 1443 bayan Hijira (14. 05. 2022 Miladiyya) a Sokoto, yayin da kuma muna kira ga gwamnati da ta binciki ayyukan jami'an tsaron da kuma gurfanar da waɗanda aka samu da hannu a gaban ƙuliya. 

c. Rundunar ‘yan Sandan Najeriya da Hukumar Jami’an Tsaro na Farin Kaya da sauran hukumomin da abin ya shafa, su yi bincike cikin gaggawa tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a tashar dandalin sada zumunta na zamani na YouTube mai suna JARUMA HAUSA TV a gaban shari’ah, waɗanda suka mayar da babbar aikinsu shi ne yin kalamai na wulakanci a kan mutane masu mutunci kuma fitattun Musulmi kamar wanda ya kafa Daular Usmaniyya, Shaikh Usmanu bn Fodiyo (Allah Ya yi masa rahama), Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Mai Martaba Sarkin Musulmi, Sarakuna masu yawa da manyan Malaman Musulunci da dama. Ya kamata a yi hakan don gujewa tada zaune tsaye na Addini.

d. Shuwagabannin Musulmi waɗanda suka ƙi kare martabar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam, kuma suka ƙi tsayawa tsayin-daka wajen kare hakkoƙin Musulmi a bisa kowane dalili ne, su sani cewa Musulunci shi ne dalilin girmansu, kuma idan sun nemi ɗaukaka. daga wajen sa, lalle Allah Ta’ala zai wulakanta su.

e. Ya kamata shuwagabannin Kirista, don neman zaman lafiya, su fito fili su yi wa’azi ga mabiyan su a kan a daina ɓatanci , su kuma ilimantar su cewa ɓatanci ya saɓa wa littafan Addininsu, kuma abu ne da ke kunna wutar fitina wadda za ta fara laƙume mai laifin kafin ta kai ga wasu.

f. Muna kira ga Malaman Addinin Musulunci da Limamai da masu wa'azi da su ƙara himma wajen wayar da kan al'umma Musulmi da wadanda ba musulmi ba, game da kyawawan halaye da tarihin rayuwar Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) da sauran Annabawan Allah (tsira da Amincin Allah su tabbata a gare su), a matsayinsu na mafi daukakar mutane masu babbar daraja, wadanda suka cancanci dukkan girmamawa. 

g. Haka nan, muna kira ga dukkan Musulmi da su kwantar da hankulansu, su kiyaye doka, su nisanci duk wani abu da zai haifar da hargitsi, tare da ci gaba da koyi da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a dukkan ɓangarorin rayuwar su.

9. Daga ƙarshe muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ƙara mana so da girmamawa da koyi da ManzonSa Muhammad ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi); Ya tabbatar da mu akan tafarkinsa duniya da lahira; Ya shiryar da masu ƙiyayya da shi bisa jahilci zuwa ga tafarki madaidaici kuma Ya kawo zaman lafiya da wadata ga al’ummarmu, lallai Shi mai ikon yin haka ne.

Sa Hannu

  

Prof. Isa Muhammad Maishanu (Shugaba na Riƙo) da Mal. Muhammad Usman Ali (Sakatare na Riƙo)

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow